Yaushe Obasanjo ya fara yi wa shugabannin kasa baki?

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A ranar Litinin ne tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya rubuta ga Shugaba Muhammadu Buhari wasika a karo na biyu tun hawansa mulki a 2015, inda ya gargade shi da cewa “Najeriya na daf da fadawa wani wawakeken rami mai cike da hadari kuma shugaban kasar ne kawai zai iya dakatar da wannan mummunan bala’i”.

A kan haka ne BBC ta yi waiwaye kan wani bidiyo da ta fara wallafa shi a watan Janairun 2019, lokacin da Obasanjon ya rubutawa Shugaba Buharin wasikar farko, inda ta yi duba kan

Waiwaye kan bidiyon

Masana harkokin siyasa sun ce wasikar da tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari tamkar wata al’ada ce ta tsohon shugaban.

A farkon makon nan ne Cif Obasanjo ya rubuta wa Shugaba Buhari budaddiyar wasika inda ya soke shi bisa abin da ya kira rashin iya shugabancinsa.

Mr Obasanjo ya ce Shugaba Buhari ba zai iya fitar wa Najeriya kitse a wuta ba don haka bai cancanci yin wa’adi biyu na shugabancin kasar ba.

Daga nan ne tsohon shugaban ya yi kira a gare shi da ya ajiye mulki idan wa’adinsa na farko ya kare sannan ya bi sahun tsoffin shugabannin kasar wajen bayar da shawarwari kan yadda za a gyara Najeriya.

Wani mai sharhi kan harkokin siyasa Bashir Baba ya shaida wa BBC cewa tsohon shugaban kasar “tamkar tauraruwa mai wutsiya ce, wacce Hausawa kan ce ganinki ba alheri ba.”

“Wannan ba shi ne karon farko da wannan dattijo ke sukar shugabannin da ke mulki ba. Ya soji Alhaji Shehu Shagari da Janar Ibrahim Babangida da Janar Sani Abacha. Sukar da ya yi wa Abacha ce ta sa aka daure shi.

“Bayan ya sauka daga shugabancin kasa a shekarar 2017, Marigayi Umaru Musa ‘Yar Adua, wanda shi ya dora shi a mulki, ya hau sai da Cif Obasanjo ya soke shi. Haka kuma ya soki Dr Goodluck Jonathan,” in ji Bashir Baba.

Ya kara da cewa kusan duk lokacin da Cif Obasanjo ya soki shugaba mai-ci shi ne da gaskiya, amma duk da haka “shi kansa bai iya yin mulki irin wanda yake son wasu su yi ba. Da alama yana ganin shi ne ya fi kowa iya mulki.”

Sukar da Obasanjo ke fitowa fili ya yi wa shugabannin kasashe, sau da yawa, na nuni ga karatowar karshen wadannan gwamnatoci.

Wannan layi ne

Mulkin Shehu Shagari

shagariHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Shugaba na farko da Obasanjo ya yi wa irin wannan wasika shi ne Alhaji Shehu Shagari wanda ya yi mulkin Najeriya daga 1 ga Oktoba 1979 zuwa 31 ga Disambar 1983.

‘Yan watanni bayan hawansa mulki a wa’adi na biyu a 1983, Obasanjo ya yi suka ga Shehu Shagari kan tabarbarewar tattalin arziki inda ya ce hakan ya jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali.

Ya kuma yi korafin cewa cin hanci da rashawa sun yi katutu a kasar.

Wannan suka da Obasanjo ya yi, ya zama kamar usur ne aka hura don kuwa ‘yan makwanni bayan haka rundunar soja ta yi wa gwamnatin Shagari juyin mulki.

Wannan layi ne

Mulkin Janar Ibrahim Babangida

Obasanjo bai kyale Babangida ba a lokacin da ya ke mulki.

Babngida ya kaddamar da sabon shiri a tattalin arzikin kasar na Structural Adjustment Programme wanda ya kara radadin wahalar da talakawa ke fuskanta a kasar.

Obasanjo ya ari bakin talakawa ya ci masu albasa inda ya soki wannan mataki na gwamnatin Babangida.

Bayan da aka soke zaben 12 ga watan Yunin 1993 wanda Cif Moshood Abiola ya lashe, Obasanjo ya ci gaba da sukar gwamnatin Babangida har ya sauka daga mulki ran 27 ga Agustan 1993 bayan shekara 8 yana mulkin soja.

Wannan layi ne

Mulkin Janar Sani Abacha

Har ila yau, sukar da Obasanjo ya saba yi wa shugabanni ba ta tsallake Janar Sani Abacha ba.

A lokacin da ya ke wani jawabi a lokacin mulkin Abacha, Obasanjo ya bayyana gwamnatin a matsayin marar alkibla.

Haka ma a wata hira da yayi da BBC, ya zargi gwamnatin Abacha da almubazzaranci da albarkatun kasa.

Sai dai ba kamar Babangida ba da ya yi kunnen uwar shegu da sukar Obasanjo, Abacha ya mayar masa da martani ta hanyar bayyana cewa Obasanjo na da hannu a wani yunkurin juyin mulki.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 88

Wani kwamitin soji da Abacha ya kafa, ya kama Obasanjo da laifi aka kuma yanke masa hukuncin dauri.

Ya kasance a gidan kaso har sai karshen mulkin Janar Abacha, da ya mutu a watan Yunin 1998.

Janar Abacha ya daure Cif ObasanjoHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionJanar Abacha ya daure Cif Obasanjo
Wannan layi ne

Mulkin Umaru Musa ‘Yar’adua

Olusegun Obasanjo ya tsunduma harkar siyasa bayan sakinsa, inda ya shiga jma’iyyar PDP kuma ya tsaya takarar shugabancin Najeriya.

Ya hau mulki ran 29 ga Mayun 1999 ya sauka a Mayun 2007 inda Umaru ‘Yar’adua ya gaje shi.

Takun sakar da ke tsakanin ‘Yar’adua da Obasanjo ya bayyana ne saboda rashin gamsuwar da Obasanjo ya yi da mulkin ‘Yar’adua.

Don bayyana haka, Obasanjo ya rubuta wa gwamnatin ‘Yar’adua wasika tun a farkon mulkinsa, inda ya ce lallai ne shugaban ya zage dantse a yadda ya ke tafi da ayyukansa.

Sai dai wasikar ta karfafa rashin jituwa tsakanin Obasanjo da magajinsa.

Sai dai Shugaba ‘Yar’adua ya kasance marar koshin lafiya.

A lokacin da ya tafi Saudiyya don neman magani, ‘Yar’adua bai mika mulki yadda doka ta tanada ba ga mataimakinsa kuma hakan ya jefa najeriya cikin rikici.

Obasanjo da sauran shugabanni sun ziyarci ‘Yar’adua a Saudiyya inda yake jinya.

Dawowar Obasanjo ke da wuya, ya bayyana wa manema labarai halin da ‘Yar’adua ke ciki da kuma bukatar a fara neman wanda zai gaje shi.

Wannan tatagurzar ta kai ga mataimakin ‘Yar’adua, Goodluck Ebele Jonatha zama shugaban Najeriya.

Wannan layi ne

Mulkin Goodluck Jonathan

jonathan buhariHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES

Ranar 2 ga watan Disambar 2013, Obasanjo ya rubuta budaddiyar wasika ga Goodluck Jonathan.

A wasikar wacce ya yi wa taken “Kafn Lokaci ya Kure”, Obasanjo ya bayyana cewa ya yanke shawarar rubuta budaddiyar wasikar ne saboda a baya ya rubuta wa Jonathan wasiku hudu cikin sirri kuma bai ba shi amsa ba.

Ya ce ya zama dole ya rubuta wasikar saboda ya ga alamun cewa gwamnatin Jonathan na da kamanni da gwamnatin Abacha.

Sannan ya yi kira ga Jonathan da ya dage wajen ganin najeriya bata rabu ba tsakanin musulmi da kiristoci ko kuma ‘yan kudu da ‘yan Arewa.

Jonathan ya amsa wasikar inda ya musanta duk wani bayani da Obasanjo ya yi a tasa wasikar.

A wasikar da Obasanjo ya rubuta wa Buhari, bai boye manufarsa ba, ta ganin ya yi dukkan mai yiwuwa don ganin Buhari bai koma mulki a 2019 ba.

Sai dai abun tambaya a nan shi ne, shin Obasanjo zai yi nasarar tuge Buhari kamar yadda ya yi wa Jonathan?

Wannan layi ne

Shugabannin da Obasanjo ya soka

  • Shehu Shagari ne shugaban da Obasanjo ya fara suka jim kadan bayan da ya mika masa mulki
  • Ya soki Janar Buhari loakcin yana mulkin soja
  • Ya soki Janar Ibrahim Babangida
  • Ya kuma taba sukar Janar Sani Abacha
  • Obasanjo ya kuma soki Ummaru Musa ‘Yar aduwa
  • Kazalika ya soki Goodluck Jonathan
  • Sai kuma sukar da ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari har sai biyu a mulkinsa na farar hula tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019.
Wannan layi ne

Shugabannin da Obasanjo bai taba suka ba

  • Janar Abdulsalami Abubakar
  • Cif Ernest Shonekan

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.