Labarai

Yau Sarkin Kano Zai Biya Wa Fursunoni Tara

A yayin da watan azumin Ramadan ya ke karewa, a yau ne Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, zai ziyarci gidan yarin Kano, domin biya wa fursunonin da a ka daure bisa laifin cin tara, saboda a sake su. Rahotanni daga fadar sarkin sun tabbata wa da LEADERSHIP A YAU cewa, tun a makon jiya Mai martaba Sanusi II ya yi niyyar a sallami fursunonin da ke daure bisa kasa biyan kudaden tarar da kotuna su ka yi mu su a ziyarar da ya kai gidan yarin, amma kurewar lokaci na rashin samun damar tattaunawa da tantance wadanda a ke bi bashin ya sanya sarkin ya dage aniyarsa tasa har zuwa yau Litinin, wacce ta zo daidai da karshen watan azumin.

Majiyar fadar ta tabbatar ma na da cewa, sarkin ya yi nufin hakan ne, don tausaya wa ga talakawansa marasa galihu, musamman a irin wannan wata mai alfarma. Wasika: Kirkirar Sababbin Masarautu Zai Kawo Rabuwar Kai A Jihar Kano Ne Datsawa ko kacalcala Masarautar Jahar Kano mai mai dadadden tarihi da darajja a duniya bakidaya da wani dan siyasa, wanda zai rike kujerar gwamnan tsawon shekara takwas kacal, ya koma kauyensu, wato Audu Ganduje ya yi, saboda watakila ya na son cimma wata bukata tashi ta siyasa hakan abin tir da Allah wadai ne, duba da ganin Kanawa shekaru aru-aru su na zaune uwa daya uba daya.

Wato matsayin tsintsiya mai madaurinki daya, kuma da yakinin su na da kudiri ko fatan su cigaba da zama a haka. Sai dai kash! wannan dan siyasar ya dauko hanyar raba waccan tsohuwar tafiya da su ka dade su na yi tun kaka da kakanni, domin datsa muhimmiyar masarauta, kamar ta Kano, hakan wani babban cikas ne, ba wai a jahar kadai ba, a kasa ne bakidaya, domin tamkar ya raba kawunansu ne.

Wani abin damuwa da daure kai shi ne, tun da dan dagajin siyasar ya fara shirin ko yunkurin rar-raba masarautar har ya kammala ba mu ji wani kusa ko mai fada-a-ji daga gwamnatin tarayya da ya taka ma sa burki ba, wanda hakan ya sa wasu jama’a na kallon cewa, tsintsiya daya ba ta iya yin shara.

’Yan siyasa ya kamata a kullum ku rika kokarin samar da hanyoyin da za su rika hada kawunan jama’a, ba wai hanyoyin da za su rika raba kawunansu ba. Ku sani sarakuna da malamai iyayen jama’a ne.

Ya kamata ku rika mutumta su. Su kuma sarakunan da malaman ya kamata su rika tsayawa a matsayinsu; kada kwadayin abin duniya ga ’yan siyasa ya sa ku zurma ‘ya’yanku, kannenku, jikokinku da dalibanku, domin da yawa kun fi su ilimin addini da na zamani gami da wayewa, wanda kuma bai kashe mu ku kishirwa ya sa ku rika zubar da mutumcinku da kimarku.

Mu kuma da ku ke yiwa jagoranci ba dadin hakan za mu ji ba. Da fatan Allah Ubangiji ya kara hada kawunanmu a wuri daya, ya kuma kawo wa kasarmu zaman lafiya. Shugabanninmu da ke kokarin raba kawunanmu, ya Allah ka shirye su, idan masu shiryuwa ne.

Idan kuma ba masu shiryuwa ba ne, kai ma na maganinsu. Haruna Muhammad Katsina shi ne shugaban kungiyar Muryar Jama’a. Za a iya tuntubar sa a wadannan layikan waya guda biyu: 07039205659, 08055887110.