-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Yau Rikici Ya Barke A Majalisar Dattawa Tsakanin Sanatoci Inyamurai Da Na Arewa.


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rikici ya barke a Majalisar dattawan Najeriya a yau Talata, 11 ga watan Disamba yayinda sanatoci sukayi cacan baki kan tabbatar da sabbin mambobin hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC.

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sunayen sabbin mambobin hukumar uku ga majalisar dattawa a watan Yulin 2016. Mambobin sune Ndasule Moses, Lawan Mamman, Galadanci Najib da Adeleke Adebayo Rafiu.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 660

- Advertisement -

Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan yakin da rashawa, Chukwuka Utazi, ya mika aikin kwamtinsa ga yan majalisa domin tabbatar da su.

Ana cikin magana sai Sanata Victor Umeh ya nuna bacin ransa kan wadanda Buhari ya nada saboda an nuna bangaranci a dukkan nade-naden da akayi a kwanakin nan, an mayar da yankin kudu maso gabas saniyar ware.

Ya bayyana cewa yayinda shugaban EFCC, Ibrahim Magu dan arewa maso gabas ne, sakataren hukumar, Olanipkekun Olukoyede, dan yankin yarbawa ne kuma wadannan sabbin kuma yan arewa ne. Saboda haka, kada a tabbatar da sunayen har sai an sake duba wannan lamari.

Wannan ya jawo cece-kuce cikin yan majalisan inda shugaban masu rinjaye, Ahmed Lawan, yace majalisar ta cigaba aikinta ta tabbatar da su, sanatocin yanki Igbo sunce sam ba za’ayi ba. Kawai sai yan majalisan suka rikita majalisar da zage-zage da hayaniya.

Shugaban majalisar, Bukola Saraki, ya yi kokarin kwnatar da kuran amma ya gaza. Daga baya dole aka tashi daga zaman majalisa.

Madogara: Rahma Tv
Mubarak Musa Al-Mubarak

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: