Labarai

A Yau Ne Za A Fara Jigilar Maniyyatan Aikin Hajjin Bana

A Yau Ne Za A Fara Jigilar Maniyyatan Aikin Hajjin Bana

A yau Lahadi ne, aka tsara za a fara aiki jigilar maniyyata aikin hajjin bana inda aka kaddamar da aikin a Babban birnin tarayya Abuja.

 

Shugaban hukumar kula da filayen saukar jiragen sama ta kasa(FAAN), Injiniya Sakeh Dunoma ya kalubalanci maniyyata kan su rika fitowa kan lokaci idan har an neme su don gudun kada jirgi ya bar su.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa hukumar FAAN ta kammala duk wasu shirye shirye ba a samu cikas a yayin jigilar maniyyatan ba inda ya nuna cewa kamfanonin jiragen saman fasa su yi aikin jigilar su ne ; FlyNas Airline, Azman Airline da kuma Max Air.