-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Yau A Najeriya `yan Rashawa Ake Girmamawa : Balarabe Musa Ya Caccaki Osinbajo


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Yau a Najeriya ‘yan rashawa ake girmamawa : Balarabe Musa ya caccaki Osinbajo, EFCC kan shirin karrama Ganduje da lambar yabo

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Balarabe Musa, a ranar juma’a data gabata , ya yi Alla-wadai da kambar karramawar da 2018 Africa Value Awards, suka shirya baiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a matsayin gwarzon shekara kan “shugabanci na gari da bunkasa tattalin arziki.”

A yau asabar ne dai aka shirya karrama Ganduje da wannan babban kambu.

A baya bayan nan ne dai Ganduje ya shiga tasku, sakamakon sakin wasu faya fayen bidiyo da ke nuna yadda gwamnan ke karbar cin hancin daloli daga ‘yan kwagila a wurare daban daban.

Balarabe Musa, a zantawarsa da manema labarai, ya bayyana wannan karramar a matsayin babbar alama ta cewar an mayar da cin hanci ba a bakin komai ba a kasar nan.

Balarabe Musa Ya ce: “Yanzu cin hanci ya zama ruwan dare a Nigeria.

Wanda ake zargi da rashawa shine ake karramawa, don haka ba abin mamaki bane.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

- Advertisement -

Mutanen da ake karramawar zaka same su marasa kima da daraja a idanun mutane masu mutunci. Abun da ban tsoro, hakan ya nuna kololuwar cin hanci a Nigeria.”

Da ya ke tsokaci kan cewar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo na daga cikin masu ruwa da tsaki a wajen karramawar, kasancewarsa bako na musamman a taron, Musa ya gargadi mataimakin shugaban kasar da ya nisantar da kansa da Ganduje.

Ya kara da cewa, “Shi (Osinbajo) ba ya jin kunyar hakan.

Ba ya jin kunyar tarayyarsa da Ganduje wanda ake zarginsa tare da hujjoji karara kan cin hanci da rashawa.

“Mai makon a tsaya a yaki cin hanci da rashawa, an buge ana karrama masu cin hancin. Sam, ba a jin kunyar cin hanci a kasar nan.

Na daga cikin wani hali da yayi katutu a tsakanin masu mulki a kasar. Ba wai wani abu bane da ake jin kunyar aikatawa.”

Dangane da gazawar EFCC na tuhumar gwamnan, Musa ya bayyana cewa ma damar mutum na da kudi da karfin iko, to kuwa ya fi karfin a kira shi da mai cin hanci, yana mai cewa EFCC na daga cikin masu kara iza wutar

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: