Labarai

Yarinya ‘Yar Shekara 14 Ta Zama Gwamnar Jihar Bauchi Na Rikon Kwarya

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya sanya wata yarinya kan kujeran mulkin jihar Bauchi na wani dan lokaci yarinyar mai shekara 14, Aisha katagum ta samu damar shiga tarihi na deke kujerar a ziyarar da suka kawo gidan Gwamnatin jihar Bauchi cikin bikin Ranar’ Ya mace na kasa da kasa 2021. da hukuma (IDGC) ta shirya.

An umarci yarinyar mai shekaru 14 ta yi rikon kujerar Gwamnan jihar Bauchi na wasu mintuna Sabila da girmama wannan rana ta diyya Mace.

Bikin na wannan shekarar an yi masa taken abar ‘ya’ya mata su karbi ragamar mulki. Wanda hukumar kula da yara ta duniya (UNICEF) tare da hukumar Partners, Civil Society Group suka shirya.

Daga Lawal Muazu Bauchi
Mai taimakawa Gwamnan jihar Bauchi kan Sabbin kafofin yada labarai na zamani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: