Yarabawa Buhari Zai Mika Wa Mulki A 2023 – Osinbajo

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce mulki zai dawo yankinsu na kudu maso yamma idan Buhari ya kammala wa’adinsa na biyu.

A yayin da yake yakin neman zabe a jihar Oyo, Osinbajo ya ce Buhari zai mika wa Yarabawa mulki a 2023 idan har sun mara ma shi baya a zaben 2019, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Talla

“Zaben 2019 ya shafi al’ummar Yarabawa a kudu masu yammaci saboda babbar bukatar yankin a 2023,” in ji shi.

Osinanjo wanda ya bi gida gida da kasuwanni da sako a Ibadan da wasu sassan jihar Oyo, ya yi kira ga mutanen yankin su fito domin sake zaben Buhari.

Shugaba Buhari dai ya sha mika ragamar tafiyar da kasa ga mataimakinsa Osinbajo a duk lokacin da zai je jinya kasashen waje.

Kuma yadda Osinbajo ya zartar da daukar wasu matakai kan wasu muhimman al’amurra a kasar, wasu ke ganin ya kama hanyar zama shugaban kasa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

Yana mukaddashin shugaban kasa aka kara farashin litar fetur, sannan shi ya sallami shugaban hukumar DSS, Lawal Daura.

Komawar mulki yankin kudu maso yammaci a 2023 zai dogara ne da samun nasarar Buhari a zaben 2019.

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi OsinbajoHakkin mallakar hotoNOVO ISIORO

A martaninta, babbar jam’iyyar adawa PDP ta ce tana mai ba mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo shawara da ya farka idan mafarki yake na zama shugaban kasa a 2023, domin shugaba Buhari zai sha kaye a zaben 2019 da za a yi watan Fabrairu.

“Abin dariya ne ace Farfesa Osinbajo har ya fara irin wannan tunanin bayan ba wani tasirin da Buhari zai yi bayan zaben 2019 saboda gwamnatinsa ce mafi muni a tarihin Najeriya,” in ji PDP.

BBC HAUSA

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: