- Advertisement -
Yar shekara hudu ta rasu bayan faɗawa rijiya a Kano
Wata yarinya ‘yar shekara hudu ta rasu bayan faɗawa a rijiya a unguwar Kofar Waika da ke cikin jihar Kano a arewacin Najeriya.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kwana-kwana ya fitar, na cewa al’amarin ya faru ne a ranar Litinin da rana.
Alhaji Saminu Abdullahi ya ce an sanar da su faruwar al’amarin da misalin karfe 02:05 na rana, kuma sun gaggauta zuwa ceto ta da misalin 02:20 na rana.
Sai dai a cewar jami’in lokacin da aka dauko yarinyar ta riga ta rasu.