Wata yarinya ‘yar shekara 10 da aka yi wa fyade a Indiya, wacce kuma kotun kolin kasar ta hana a zubar mata da cikin a watan da ya gabata, ta haifi ‘ya mace.
Yarinyar dai ba ta san cewa tana shirin haihuwa ba. A lokacin da take da cikin, an shaida mata cewa akwai katon dutse a cikinta ne shi ya sa ya yi girma.
An haifi jaririyar wacce ke da nauyin kilo 2.5 ne ta hanyar yi wa uwar tiyata a garin Chandigarh, da misalin karfe 3.52 na tsakar daren Laraba a agogon GMT.
Wani jami’i ya shaida wa BBC cewa, da uwar da jaririyar duk suna cikin halin lafiya.
Yarinyar ta fadi cewa kawunta ne ya yi mata fyade sau ba iyaka cikin wata bakwai da suka gabata, amma tuni an kama shi.
An gane tana da cikin ne kusan wata daya da ya wuce a lokacin da ta yi korafin cewa cikinta na ciwo, sai iyayenta suka kai ta asibiti.
A makon da ya gabata ne, Kotun Koli ta hana a zubar da cikin yarinyar kan dalilin cewa cikin ya tsufa a lokacin da aka gane, don likitoci sun ce ya kai mako 32, don haka zubar da shi na iya sa rayuwarta a hadari.
Dama kafin hukuncin kotun kolin, wata karamar kotu ma ta yanke irin wannan hukunci kan wadancan dalilan.
Add Comment