Labarai

“Yanzu-Yanzu Hukumar NCDC Ta Haramtawa Musulmai Gudanar da Cinkoson Al’umma a Cikin Masallatan Idi”

Hukumar dake hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta haramtawa al’ummar musulmi gudanar da cinkoson al’umma a cikin masallatan idi don kaucewa kamuwa ko yada cutar Covid-19.

Shugaban hukumar na kasa Chikwe Iheakweazu ne ya yi wannan gargadin yanzun nan domin tura sako zuwa ga al’ummomi kan bukukuwan sallah babba da zasu gudanar.

Ya yin da ake saura kwanaki 6 al’ummar musulmi na duniya su gudanar da Babbar Sallah layya, ita kuwa hukumar NCDC ta gargadi musulmai dasu kauracewa gudanar da cinkoson al’umma domin kaucewa kamuwa da cutar ta korona.

Hukumar ta NCDC haka ma ta bayyana cewar, kasancewar har yanzu akwai sauran cutur ga jikin al’umma tare da wata bakuwar cuta da ta bulla a kasar domin haka akwai bukatar musulmai su kauracewa duk wani abu da zai haifar da cinkoson mutane domin gujewa kamuwa da cutar don yadawa al’umma.

Mi Zaku Ce?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: