Labarai

Yanzu- Yanzu : Cutar Kwalara ta bayyana Jihar Katsina har ta hallaka aƙalla mutum 60

Daga Falalu Lawal Katsina
..jaridar The Channels ta ruwaito Cewa Akalla mutun 60 ne suka rasa rayuwarsu a faɗin kauyukan jihar Katsina bayan ɓarkewar cutar kwalara a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Yakubu Nuhu Danja, shine ya bayyana haka a wurin taron shekara-shekara na ƙungiyar likitoci (NMA).

Sai dai kwamishinan bai bayyana lokacin da suka ɗauki wannan kididdigar rasa rayukan ba.

Sai dai Kwamishinan ya bayyana cewa a halin yanzun gwamnati na duba dukkan wasu hanyoyin da za’a bi domin dakile yaɗuwar cutar a faɗin kananan hukumomin jihar 34.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: