Yanzu Nake Jin Dadin Wasa A United — Pogba

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Dan kwallon Manchester United, Paul Pogba ya ce yanzu ne yake jin dadin murza-leda karkashin kocin rikon kwarya Ole Gunner Solskjaer.

Hulda tsakanin Pogba da Jose Mourinho ta yi tsami, inda yake ajiye dan kwallon Faransa a benci, har da wasan da Liverpool ta doke United a watan Disamba.

Talla

Bayan wasan ne United ta sallami Mourinho ta kuma nada Solskjaer kocin rikon kwarya zuwa karshen kakar 2018/19.

Pogba ya dawo kan ganiyarsa karkashin Solskser wanda ya horas da shi a matasan United, yanzu kuma ya ba shi damar yin yadda yake so a cikin fili.

Wasu Abubuwan Masu Alaka

Nasan Annabi Muhammadu Shine Mutumin da Yafi Kowa a Duniya…

Talla
1 of 54

Hakan ne ya bai wa Pogba damar cin kwallo hudu ya kuma bayar da hudu da aka zura a raga, har da wadda ya bai wa Marcus Rashford ya ci Tottenham a ranar Lahadi.

United ta ci wasa shida a jere da kocin rikon kwarya Solskjaer ya ja ragamarta a karon farko, kuma biyar a gasar Premier.

Kungiyar tana ta shida a kan teburi da maki 41 iri daya da wanda Arsenal ta ke da shi mai mataki na biyar a teburin Premier.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: