Siyasa

Yanzu mun yarda za’a rantsar da Abba, amma za’a karɓe kujerar a bamu ~ APC

Yanzu mun yarda za’a rantsar da Abba, amma za’a karɓe kujerar a bamu ~ APC

 

Magoya bayan jam’iyyar APC a jihar Kano, sun bayyana cewa za’a rantsar da zaɓaɓɓen gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, a ranar 29 ga watan da muke ciki na Mayu, sai dai kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamna za ta kwace kujerar ta dawo musu da ita, duba da yadda irin haka sun taba faruwa a wasu Jihohin ƙasar nan.

 

Jaridar Kano Online News ta rawaito cewa, jigon APC kuma lauya masanin doka, Barista Sanusi Musa, ne ya basu wannan ƙwarin gwiwa, inda ya wallafa a shafinsa na Facebook, Ekiti, Edo, Ondo, Bayelsa, Kogi, Imo, Osun duk bayan an ranstar da Gwamnoni sun dan dana kotu ta sauke su.

 

Wallafa hakan ke da wuya, magoya bayan APC a Kano musamman mambobin ƙungiyar Gawuna is coming, suka cigaba da yada manufarsu ta cewa Gawuna zai zo.

 

Ya kuka kalli wannan al’amari?

 

Daga: Kano Online News

24/5/2023