Kiwon lafiya

Yanayi 4 dake sa a gane an kamu da Zazzabin Lassa, da yadda za a’ samu kariya daga kamuwa

1. Zazzabi, ciwon kirji, ciwon gabobin jiki da naman jiki, rashin garfin jiki wanda ke sa mutum yawan kwanciya.

2. Mutum zai iya fara zubar da jini ta hanci,baki,makogoro da kunburin huska.

3. Cutar na sa mutum suma.

4. Zubar da gashi daga kai ko wasu sassan jikin mutum.

Hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar.

1. Tsaftace muhalli ta hanyar kawar da beraye a cikin gida.

2. Killace duk kayayyakin abinci daga inda beraye ke shawagi.

3. Mutanen su daina baza ko kuma busar da kayayakin abinci a gefen titi saboda bera na iya bi ta kai.

4. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun kare kan su a lokacin da suke kula da wadanda suke dauke da cutar a asibitoci.