Labarai

Yan takarar shugabancin majalisar wakilai guda 7 sunyi fatali da hukuncin APC

G7: Yan takarar shugabancin majalisar wakilai guda 7 sunyi fatali da hukuncin APC

Yan majalisu guda bakwai da ke neman kujerar shugabancin majalisar wakilai ta ƙasa, sun hallara a babbar hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa dake babban Birnin tarayya Abuja, inda suka gana da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, domin bayyana masa korafinsu na rashin amincewa da zaɓin shugabannin majalisar ta goma da jam’iyyar tayi.

Masu neman shugabancin sun hada da Yusuf Gagdi, Mukhtar Aliyu Betara, Ahmed Idris Wase, Alhassan Doguwa, Sada Soli, Mariam Onuoha da Aminu Sani Jaji, inda suka ce, shugabancin majalisa na yan majalisa ne, kuma anyi rashin adalci wajen rarraba mukaman a shiyya-shiyya, saboda haka ya kamata a kyale Demokradiyya tayi halinta, kamar yadda akayi a lokacin zaɓen fidda gwani na dan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar tasu ta APC.

Tuni dai ake ta turka-turka akan kafa shugabancin majalisar tarayya ta goma, da za’a rantsar nan gaba kaɗan, inda jam’iyyar APC ta bayyana Sanata Godwill Akpabio a matsayin wanda ta ke so da kuma muradin ya zama shugaban majalisar dattijai, da Sanata Barau Jibrin a matsayin mataimakinsa, sai kuma Abass Tajuddeen a matsayin shugaban majalisar wakilai da Ben Kalu a matsayin mataimakinsa.

Tushe

#NasaraRadio

#AmanarTalaka

10/5/2023

About the author

habibjs

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.