Labarai

‘Yan Ta’addan Dajin Faskari Dake Jihar Katsina Su Ma Sun Fara Karbar Kidan Janaral A Sama

Daga Kamalancy
Da sanyin safiyar yau Laraba kimanin motocin yaki 40 dauke da sojoji rike da manyan makamai masu saurin hallaka rayuwa sun shiga dajin Ruwan Godiya. Wanda ya hada da dajin Mununu domin hallaka ‘yan ta’adda.

Sojojin sun shiga dajin tare da samun rakiyar jiragen saman yaki fiye da hudu.

Kawo yanzu dai mayakan sun dawo, inda an ga suna rera wakokin nasarar yaki, jiragen kuma suna wani irin kuka mai nuni da alamun sun karkashe rayuka.

Jinjinar ban girma ga rundunar dakaru sojojin tsaron kasar mu Nijeriya.

Ya Allah ya kara baku nasara a fagen yaki da ‘yan ta’adda.

Akwai cikakken sauran rahotan labarin na nan tafe ku kasance tare da mu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: