Uncategorized

‘Yan Shi’a sun yi jerin-gwano kan ranar Qudus a Nigeria

A shekarar 1979 aka fara yin wannan jerin-gwano a kasar Iran
A ranar Juma’a ne mabiya Shi’a a Najeriya ke bin sahun ‘yan uwansu na wasu kasashe domin gudanar da jerin-gwano don tunawa da “ranar Qudus”.
Ana yin jerin-gwano a ranar ta Qudus a kowacce Jum’ar karshe ta watan azumin Ramadana domin nuna goyon baya ga Paladinawa da kyamar Yahudawan da ke gallaza musu.
A shekarar 1979 aka fara yin wannan jerin-gwano a kasar Iran.
Sai dai an sha samun arangama tsakanin mabiya Shia da jami’an tsaron Najeriya.

Ko da a baya bayan nan an samu tashin hankalin tsakaninsu bayan rundunar sojin Najeriya ta yi zargin cewa ‘yan Shi’a sun yi yunkurin halaka Babban Hafsan sojin ka, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, sai dai ‘yan kungiyar sun musanta zargin.
Lamarin dai ya kai ga kisan ‘yan Shia da dama da kuma kama shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da manyan mataimakansa da ‘yan kungiyar.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.