-Advertisement-


‘Yan Sanda Za Su Ba Da Ladan ₦5m ga Duk Mai Masaniya Ko Kuma Karin Bayani Kan Garkuwa Da Alhaji Musa Umar,


0 205

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Katsina ta yi alkawarin ba da ladan naira miliyan biyar ga duk mai masaniya ko kuma karin bayani kan garkuwa da Alhaji Musa Umar, wanda hakimi ne a garin Daura.

Wannan na zuwa ne bayan da a kalla mutum hudu suka zo har gidansa a Daura bayan magriba suka sace shi.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Gambo Isa, ya bayyana cewa wannan ladan za a bayar da shi ne domin taimaka wa ‘yan sanda samun bayanai kan wadanda suka yi garkuwa da hakimin da kuma kokarin ganin cewa an ceto shi daga hannunsu.

Gambo ya shaida wa BBC cewa bayan sun samu labarin garkuwar da aka yi a Daura, sun yi sauri sun bi masu garkuwar inda har suka yi musayar wuta da su.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 608

-Advertisement-

Ko da aka tambayi mai magana da yawun ‘yan sandan kan ko masu garkuwa da mutanen sun fara maganar kudin fansa, sai ya bayyana cewa “ba zai iya bayyana komai ba saboda tsaro.”

An bayyana cewa Umar Musa shi ne magajin garin Daura kuma suruki ne ga dogarin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da matsalar garkuwa da mutane da kuma fashi da makami musamman a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Ko a ranar Laraba an yi jana’izar mutum 14, wadanda suka mutu sanadiyyar wani harin da wasu mahara suka kai karamar hukumar Safana a jihar ta Katsina.

Hakazalika wasu ‘yan bindiga masu satar mutane sun kai hari a wata makarantar sakandare ta mata a jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da mutanen da ba a tantance adadinsu ba.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.