‘Yan Sanda Sun Hana ‘Yan Kwankwasiyya Gudanar Da Taro A Sakkwato
Jami’an tsaro a Jihar Sakkwato sun dakatar da mabiyan akidar Kwankwasiyya gudanar da taro ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.
Magoya bayan Kwankwasiyya sun tsara gudanar da taro a yau Laraba a Kofar Rini bayan samun umurnin amincewa da gudanar da taron daga jami’an tsaro na ‘Yan Sanda da jami’an tsaro na farin kaya wato ‘Civil Defence’ amma kuma dan lokaci kadan gabanin fara taron jami’an ‘yan sanda suka dakatar da taron.
Jagoran Kwankwasiyya na Jihar Sakkwato Honarabul Malami Muhammad Galadanci Bajare ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai.
A cewarsa “Mun gabatar da takarda a rubuce ta gudanar da wannan taron mai dauke da lamba SN1/CO.SM/017.VI mun kuma samu amincewa daga Area Commander da DPO na Dadin Kowa da Shugaban Civil Defence na Karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa amma kuma daga baya ‘yan sanda suka bayar da umurnin dakatar da taron.”
Dan Majalisar wanda ke wakiltar Mazabar Sakkwato ta Arewa Ta (1) a Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato ya bayyana cewar siyasa ce kawai kashin bayan hana masu gudanar da taro. Ya ce wannan shine karo na biyu da ‘yan sanda suka hana masu gudanar da taro. “Kwamishinan ‘Yan Sanda ya gaya mana cewar mu sake rubuta takardar neman gudanar da taro zuwa ofishinsa daga nan zai duba yiyuwar amincewa ko akasin hakan kamar yadda ya bayyana mani. A matsayin mu na masu bin doka da oda ba mu yi wata jayayya ba muka bi umurni.”
A taron mabiyan na Kwankwasiyya sun tsara rarraba kayan wasannin qwallon kafa ga club- club domin bunkasa sha’anin wasanni tare da karfafa masu guiwa.
A yayin da manema labarai suka tuntubi Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Sakkwato, Mataimakin Sufuritendan ‘Yan Sanda Ibrahim Muhammad ya bayyana cewar an dakatar da taron ne bisa ga korafin da al’ummar unguwa suka gabatar saboda gudun abin da ke iya biyowa baya. Ya ce babu wani dalili na daban baya ga bukatar da jama’a suka gabatar.
A bisa ga dakatar da taron Honarabul Bajare ya jagoranci kaddamar da rabon kayan wasannin ga Kananan Hukumomi Biyu wato Illela da Sabon Birni a gidansa.
Honarabul Sama’ila Gobir shine ya wakilci Jagoran Kwankwasiyya na kasa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a wajen taron ya kuma bayyana cewar kokarin da ake yi na dusashe Kwankwasiyya tare da hana mata motsi shine ke kara daga darajar ta a fadin kasa bakidaya. Amma alhamdulillahi mun godewa Allah jama’a sun fito daga Tambuwal da sauran Kananan Hukumomi duk sun amsa kiran mu. Mun lura babu inda aka sanyawa Kwankwasiyya ido kamar Sakkwato, a sani a na iya hana mu taro amma ba za a iya hana mu akidar Kwankwasiyya ba.” Inji shi.
Shi kuwa Tsohon Dan Majalisar Tarayya Honarabul Sarki Illela ya bayyana cewar jaruman siyasa suna fuskantar kalubale wajen gudanar da siyasa wadda a yau sai an jajirce domin siyasa ba ta matsota ba ce. A yau duk Nijeriya babu mai son Kwankwasiyya tare da yi mata hidima kamar jagoran Kwankwasiyya na Jihar Sakkwato.” Ya bayyana.
Add Comment