Labarai

‘Yan Sanda Sun Ceto Dalibin Makarantar Bethel Da Wasu Mutum Biyu A Kaduna

Daga Abubakar Abba,
A bisa kokarinta na kubutar da daukacin jama’ar da masu garkuwar ke gaba da tsare su, musamman ta hanyar samun bayanan sirri da kuma kara jajircewa wajen yin sintiri, Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta sanar da cewa, ta ceto wasu mutum uku ciki har da dalibin makarantar sakandare ta Bethel a jejin kauyen Tsohon Gaya da ke a karamar hukumar Chikun cikin jihar Kaduna.

Kakakin yada labarai na Rundunar ASP Mohammed Jalige ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya rabawar da manema labarai a jiya Talata a Kaduna, inda ya kara da cewa, sauran wadanda aka sace biyun, an kubutar da su ne a kwanan baya a hanyar Kaduna zuwa Kachiya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, daya daga cikin ukun da aka ceto dan makarantar sakandare ta Bethel Baptist High da ke a Kaduna ne da aka sace da sauran dalibai ‘yan uwansa a kwanan nan tare kuma da ceto sauran biyun.

A cewar sanarwar, Zaharaddeen Ibrahim, Nura Nuhu, su ne wadanda aka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Kachiya a kwanan baya, sai kuma Abraham Aniya, daya daga cikin daliban makarantar sakandare ta Bethel Baptist.

“Ukun da aka ceto, an yi gaggawar tura su zuwa dakin duba lafiya na Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna, inda a yanzu, ake duba lafiyarsu, domin a mika su ga ‘yan uwansu.”

A cewar sanarwa,”A ranar 12 ga watan Yulin 2021 da kimanin karfe 3:40 na dare, jami’an tsaro tare da na JTF a wani sintirin ceto daura da kauyen Tsohon Gaya a karamar hukumar Chikun cikin jihar Kaduna, sun ci karo da mutum uku da aka sace suna watangaririya a jejin kuma dukkan su a jigace.”

A karshe, rundunar ta bayar da tabbacin ci gaba da kubutar da sauran jama’ar da masu garkuwar ke ci gaba da rike su a cikin koshin lafiya nan ba da jimawa ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: