Labarai

‘Yan Sanda Sun Cafke Tsohan Kantoman Karamar Hukumar Jibia Bisa Zargin Taimakawa ‘Yan Bindiga A Jihar Katsina

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta kama tsohon Kantoman Karamar Hukumar Jibia, Alhaji Haruna Musa Mota bisa zargin taimakawa tare da hadin bakin da kuma ta’addancin yan bindiga a jihar Katsina.

Kakakin rundunar SP Gambo Isa ya tabbatar wa RARIYA ta waya cewa tabbas mun kama shi bisa zargin taimakawa tare hadin baki da yan bindiga, da suka addabi wasu kananan hukumomi. Kuma tuni aka maka shi gaban kuliya domin yi masa Sharia. Tun daga wayar da ya yi da su yan bindiga, muka fara bincike, cewar kakakin.

Kama shi bai rasa nasaba da wata waya da aka nada inda aka jiyo shi yana waya da wani jagoran ‘yan bindiga, suna tattaunawa dangane da kudin da yake cewa gwamnati ta cire da abinda aka ba su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: