`Yan Sanda Sun Bude Wuta Kan `Yan Shi`a Masu Muzahara

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

‘Yan Sanda Sun Bude Wuta Kan ‘Yan Shi’a Masu Muzahara A Kaduna

Daga Bilya Hamza Dass

Talla

Rahotanni daga jihar Kaduna sun bayyana cewa jami’an ‘yan sanda sun bude wuta don tarwatsa taron Mabiya Shi’a da suka fito zanga zanga yau a garin Kaduna.

Wasu Abubuwan Masu Alaka

Hukumar Karota Ta Kama Mota Cike Da Tabar Wiwi

Talla
1 of 661

Wani ganau dake wajan da abin ya faru ya bayyana yadda abin ya faru a daidai Kano Road, inda ya ce “lokacin da ‘yan Shi’a suka fito suna dauke da hotuna a cikin su akwai maza da mata, sai ga jami’an ‘yan sanda suka fito a motoci suna kokarin dakatar da su, bayan sun ki sai suka fara jefa barkonon tsohuwa (tiyagas) cikin taron nasu daga baya suka fara harbi da harsashi”

Majiyar ta tabbatar mana da an tarwatsa taron da tiyagas da harbi da harsashi amma ba a samu labarin an kashe wani ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

‘Yan Shi’an sun fito ne a daidai lokacin da Malamin su ke cika shekaru 3 a tsare a hannun gwamnati tun watan Disambar Shekarar 2015.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: