-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Yan Sanda A Najeriya Sun Ce Yin Jima’i Cikin Mota A Bainar Jama’a Ba Laifi Ba Ne.


1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

‘Yan sanda a Najeriya sun ce yin jima’i cikin mota a bainar jama’a ba laifi ba ne.

Babban jami’in ofishin sauraren korafin jama’a na rundunar ‘yan sandan ne Abayomi Shogunle ya fadi haka a yayin da yake amsa tambayoyi a Twitter.

An tambayi jami’in ne “ko laifi ne yin jima’i a cikin motarsa?” Sai ya ce “ba laifi ba ne” amma idan an kiyaye wasu sharudda.

Jami’in ya ce “jima’i cikin mota ba laifi ba ne a Najeriya, idan wurin da ake yi ba wurin ibada ba ne, kuma wadanda ke yi sun haura shekara 18”.

“Kuma da yardar dukkanin bangarorin da ke aikatawa, kuma Mace da Namiji ne.”

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 657

- Advertisement -

Ya kuma ce idan mutum har na fuskantar barazana a yayin aikata jami’in a mota, yana iya sanar da ‘yan sanda.

Wadannan bayanan na jami’in ‘yan sandan ya ja hankali sosai a kafofin sada zumunta, inda ya samu tsokacin mutane sama da dubu 100.

Kalaman sun janyo yabo da suka, yayin da wasu ke cewa ba dukkanin ‘yan sanda ba ne suke sane da haka, domin sun sha kame mace da namiji da suka kebe mota.

Masu suka kuma na cewa hakan ya saba wa al’adar tarbiya a Najeriya.

Za a dai ci gaba da muhawara kan wannan batu a kasar.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: