Labarai

Yan sanda a Kano sun gayyaci Abduljabbar Kabara

Rundunar yan sandan jihar Kano ta gayyaci sheikh Abduljabbar Kabara domin ya bayyana a gabanta bisa wani korafi da Dr. Abdullahi Saleh Pakistan yayi na cewa Abduljabbar din yana barazana ga rayuwar sa.

Tun a watannin baya ne Dr. Pakistan ya shigar da kara ga rundunar yan sandan akan zargin.

A hirar da yayi da manema labarai, Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa a ranar Litinin malamin zai kai kansa ofishin’yan sanda dake Bompai.

Wannan na zuwa ne awanni kadan bayan kammala zaman mukabalar da akayi tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da ragowar malaman da suke kalubalantar sa wadda aka yi a Kano a ranar Asabar. 10 ga watan Yuli.

Haarun

Haruna Lawan Usman is a certified Animal Health and Production Technologist, with more than 4 years experience in Animal Health and Production Technology.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: