-Advertisement-


Yan Najeriya da India sun yi fim kan soyayya


0 1,890

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wani fim mai suna ‘Namaste Wahala’ da aka hada gwiwa wajen shirya shi tsakanin taurarin fina-finan Indiya da takwarorinsu na Najeriya ya ja hankalin ‘yan kallo.

Za a soma nuna fim din ne ranar 24 ga watan Afrilun 2020.

Tauraruwa Ini Dima-Okojie da tauraron fina-finan Indiya Ruslaan Mumtaz sun yi fim din “wanda yake bayar da labarin wasu masoya da ke nuna al’adun kasashen biyu”.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 317

-Advertisement-

Fim din ya ja hankalin masu kallo inda suka yi ta tsokaci.

“Fina-finan Najeriya sun hada gwiwa da na Indiya? Wannan abu ya yi armashi, kuma shi ne fim irinsa na farko,” a cewar wani mai amfani da Twitter.

Sauran taurarin da za su fito a fim din sun hada da; Richard Mofe Damijo da Joke Silva da Osas Ighodaro da mai barkwancin nan broda shaggi da mawaki M.I Abaga da dai sauran su.

Wanda ya bayar da umarni a fim din ya ce an dauki fim di ne a Najeriya da Indiya.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.