Rahotanni daga Najeriya sun nuna cewa karin ‘yan matan da aka sace daga makarantar Chibok a 2014 sun tsere daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.
Mahaifin wata tsohuwar dalibar Chibok din ya shaida wa manema labarai cewa ya yi magana da ‘yarsa wadda ta tsira.
Ya ce sun yi magana da ita ta waya bayan da suka kubutu inda take ta kuka.
Bayanai na cewa ita da wasu da aka sace a Chibok da kuma wasu yankunan sun tsere ne bisa dukkan alamu saboda farmakin da sojoji suke kai wa ‘yan Boko Haram.
Matan sun tsira ne kwanaki kadan bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauya manyan hafsoshin tsaron kasar.