Labarai

Yan matan chibok 2 da aka kuɓutar sun hadu da shugaban amurka

Yan matan sun hadu da Donald Trump a fadar shugaban kasa na white house tare da ɗiyar shi

Shugaban kasar amurka ya karbi baƙoncin yan matan chibok 2 da aka kuɓutar a fadar sa ranar laraba 28 ga watan Yuni 2017.

Joy Bishara (mai shekara 20) da Lydia Pogu (mai shekaru 19) na cikin yan matan da yan ta’ada Boko haram suka yi garkuwa da su daga makaranta a garin chibok dake jihar Borno.

Shugaban kasa Donald Trump ya karbi baƙoncin su tare da ɗiyar sa Ivanka Trump.

Bayan kuɓutar dasu da sojoji suka yi daga dajin sambisa, yan matan sun koma garin virginia dake amurka don cigaba da karatun su wadda har ma sun kammala karatu a canyonvile christian Academy.

Zasu cigaba da karatu a jami’ar Southeastern universitydake garin Florida lokacin da aka bude karatu

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.