Labarai

Yan Majalisar Tarayya za su yi watandar motocin naira biliyan 6.1

Majalisar Wakilai ta tarayya, za ta yi watandar manyan motocin alfarma samfurin Peugeot 508, ga ilahirin mambobin ta su 360. An kiyasta kudin jimlar motocin har naira biliyan 6.1.

 

Kakakin majalisar, Abdulrazak Namdas, ya bayyana cewa tuni har wakilai 200 sun karbi na su motocin cikin watannin da su ka gabata. Ya ce su 360 din nan kowa zai samu daya.

Tuni dai ‘yan Najeriya ke ta yin tir da Allah wadai da wannan watandar motoci da ‘yan majalisa ke yi wa kan su. Wasu da dama sun fara kartar kasa, su na shan alwashin cewa ‘yan majalisar su duk sun ci taliyar karshe, ba za a sake zaben su ba, tunda aljifansu su ka sani, babu ruwan su da matsalar talakawan da su ka zabe su.

Dukkan kudin wadannan motoci dai za a tatse su ne daga jikin ‘yan Najeriya da sunan kudaden haraji daban-daban. Kowace mota daya dai ta tashi a kan naira miliyan 17.

Wannan watanda ta mambobin tarayya ce, babu sanatoci a ciki.

 

Source PMhausa

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.