Siyasa

Yan Majalisar Dattawan da ba su da kudiri ko guda cikin shekaru 2

Wasu Sanatocin dai shiru ka ke ji tun rantsar da su

– Guda 3 ba su kawo wani kudiri ba har yanzu tun 2015

– Jaridar Daily Trust ta kasar tayi wannan dogon bincike

Bincike da Jaridar Daily Trust tayi ya nuna cewa akwai wasu Sanatoci 3 da har yau ba su kawo kudiri ko daya tak ba daga lokacin da aka rantsar da wannan Majalisa zuwa yau fiye da shekaru biyu.

 

1-Danjuma Goje

Daga cikin wannan jerin akwai Sanatan Jihar Gombe na tsakiya karkashin APC wanda kuma tsohon Gwamnan Jihar ne. Watanni 26 kenan har yau Goje bai kawo wani kudiri ba. Danjuma Goje na cikin masu neman kujerar Shugaban Majalisar Dattawa.

2-Bukar Abba

Sanata Bukar Abba Ibrahim shi ma tsohon Gwamna ne kuma yake wakiltar Arewa maso Yammacin Yobe karkashin Jam’iyyar ANPP zuwa APC tun 2007. Cikin shekaru biyun nan dai Bukar Abba bai kawo wani kudiri a Majalisar ba. Kwanaki dai aka samu wani bidiyon babban Sanatan tare da wasu ‘Yan mata a wani irin hali.

3. Yele Omogunwa

Sanata Omogunwa kadai ne Sanatan Kudu kuma wanda ba tsohon Gwamna ba a wannan sahun. Omogunwa na wakiltar Kudancin Jihar Ondo a Majalisar Dattawa. Kawo yanzu babu kudiri ko daya daga Sanata Omogunwa.