Labarai

‘Yan Kwangilar Wargaza Nijeriya Suna Fahimtar Yaren Da Kyau

Yau a birnin Lagos an yi zazzafan arangama tsakanin dakarun ‘yan sanda da mutanen boka Sunday Igboho wadanda suka fito zanga-zangar neman kafa Kasar Yarbawa zalla Oduduwa.

Boka Sunday Igboho ya bace bat tun bayan da dakarun DSS suka mamaye gidansa, mabiyansa ne yau suka fito zanga-zanga, sai dai abin bai zo musu da dadi ba, domin ‘yan sanda sun kama na kamawa, sun tarwatsa sauran.

Ku dubi hoto na farko, an kamasu da kayan tsafi a jikinsu, kayan tsafin bai hana ‘yan sanda samun nasara a kansu ba.

Idan da mabiya shafin Datti Assalafiy zasu tuna lokacin zanga-zangar ENDSARS nace mutanen da suka hadu suke wannan zanga-zanga da wadanda suke daukar nauyinsu da goyon bayansu, matsafa ne, ‘yan damfara, masu goyon bayan auren jinsi, da miyagun mutane masu aikata manyan laifuka.

Hakika tsageru a kudancin Nigeria suna fahimtar magana da yaren da duka fi ganewa, yana daga cikin kuskuren da Gwamnatin Nigeria tayi a farko na lallabarsu, amma yanzu kam an gyara kuskuren.

Allah Ka taimaki jami’an tsaro akan tsageru, Ka bamu zaman lafiya a Kasarmu Nijeriya. Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Daga Datti Assalafiy

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: