Kannywood

'Yan Kannywood sun musanta zargin luwadi

Adam Zango a lokacin da yake rantsuwa da Al-qur’ani cewa shi ba dan luwadi ba ne.
Wasu fitattun jaruman Kannywood sun nesanta kansu da zarge-zargen da ake yi wa ‘yan fim na yin luwadi.
Tun bayan da gwamnatin tarayya ta soke shirin gina babbar farfajiyar fim a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ne dai aka rika yin ce-ce-kuce tsakanin wasu ‘yan fim da malamai, wadanda su ne suka taka rawa wajen ganin an hana gina farfajiyar.
An ambato wasu malaman na cewa wasu ‘yan fim din ‘yan luwadi ne, yayin da wasu ‘yan fim din suka rika yin gugar-zana ga malaman. 
Sai dai da alama batun zargin luwadin da aka yi wa ‘yan Kannywood din ya shiga kunnen jama’a, lamarin da ya harzuka ‘yan fim din.
A wata hira da fitaccen jarumi Adam A. Zango ya yi da gidan talabijin na DITV da ke Kaduna, ya musanta zargin yin luwadi.
Jarumin ya dafa Al-Qur’ani, sannan ya sha rantsuwa cewa bai taba yin luwadi ba, kuma shi ma ba a taba yi da shi ba, yana mai cewa idan har kalamansa babu gaskiya a ciki, Allah “ya halaka shi”.
Shi ma jarumi Baban Chinedu, a wani bidiyo da ya fitar, ya musanta zargin.
Ya kara da cewa, “Wallahil azimun! Wallahil azimun ni ban taba luwadi ba, kuma ba a taba luwadi da ni ba!”
Abokinsa ma, Mustapha Badamasi, wanda aka fi sani da Naburaska, ya caccaki mutanen da suke yi musu kazafi, yana mai cewa nan gaba kadan zai fito da shaidun da za su tozarta mutanen.
Su dai masu harkar fina-finan na da farin jiki musamman a wurin ‘yan mata da kuma matasa, sai dai kuma suna da bakin jini a wurin wasu al’ummar, wadanda ke musu kallon masu lalata al’adun Hausawa. 
Bbchausa