Labarai

Yan Jarida Sunyi Kira Da Kada A Rangwatawa Barayin Gwamnatin Neja

Kungiyar Yan Jarida ta Kasa reshen jihar Neja tayi kira ga gwamnan jihar Abu Lolo kada ya raga ma duk wani Jami’in gwamnatin jihar da aka samu da wadaka da dukiyar al-ummah daga kan ma’aikata har zuwa kan yan siyasa, sunce hakan shine sanadiyyar rashin samun cigaba a jihar tun daga lokacin da aka samar da jihar a shekara 1976.
Kungiyar ta bayyana haka cikin wata takardar bayan taro da ta fitar bayan taron kungiyar na jiha da ta gudanar a dakin taro na IBB Pen House.
Kungiyar ta ce duk wadanda aka kama da laifi na cin hanci da rashawa kada kawai a fito fili a fada ma al-ummah, a kai karar mutum zuwa kotu domin ya fuskanci hukunci sharia.
Bisa hakane, kungiyar tayi kira ga gwamnan da yayi kokarin toshe kafofin cin hanci, sannan ya bullo da wata hanyan da zaayi amfani da ita wajen gano wadannan maaikatan da yan siyasan masu cin rashawa.
Matakin da Kungiyar ta dauka ba zai rasa nasaba ba da miliyoyin kudin da aka gano daga Hukumar fensho ta jihar inda manyan maaikatan gwamnati 30 ke da hannu a cikin laifin sannan anna ganin cewa za’a yafe ma su laifin da suka aikata.
Ga hoton ‘yan kungiyar jarida reshen Neja tare da kwamishinan lafiya na Neja, Mustapha Jibrin a wani taro a shekaran 2016.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.