-Advertisement-


Yan Jarida Sunmin Karya Kan Maganar Dubu 1 Da Zaa Turomin -Rarara


0 514

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Salisu Magaji Fandalla’fih

-Advertisement-

-Advertisement-

Fitaccen mawakin nan Dauda Kahutu Rarara yayi Zargin cewa yan Jarida sun masa karya kan maganar dubu daya da yace a tura masa inda yace asalin abinda ya fada ba shi yan jaridun suka fada ba.

Mawakin ya bayyana hakane cikin wani Video inda ya zargi yan jaridun Nigeria da cewa sun sauya asalin abinda ya fada kan tura masa kudi da yace ayi domin yiwa Buhari waka.

A cewar sa shi baice ya daina yiwa Buhari waka ba, amma wasu gidajen Jaridun suka ce yace bazai kara yiwa Buhari waka ba sai an tura masa Kudi, wasu kuma sukace yace ya daina yiwa Buhari waka.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 614

-Advertisement-

Rarara yace ni bance haka ba yace abinda nace shine, wadanda suke Furo-Faganda cewa yanzu farin jinin Buhari ya ragu sai nace to ni na gamsu da Buhari kuma na gamsu har yanzu yana da niyyar gyara Nigeria, kuma ni ban yarda cewa farin jinin sa ya ragu ba dan haka zamu nunawa musu tinanin haka cewa karya suke.

Yace shi yasa nace, to ni kuma inada ayyukan Buhari wanda nasan yayi wadanda inna fadesu duk ma masu cewar baya aiki zasu dawo su yarda lallai Buhari ya taimakesu.

Yace to shiyasa nace wannan waka da zanyi Talakawa ne zasu bada kudin su ayi don a nunawa masu cewa farin jinin Buhari ya ragu karya suke.

Yace kuma nima nasa gudun mawata na dubu biyar, cikin account din dan haka indai kana tare da Buhari kaima ka turo naka sannan in ka turo ka sanar cewa kaine, yace indai mukai wannan wakar dukma mai cewa Buhari bai aiki ba saiya dawo ya bi. – Inji Rarara

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.