Labarai

Yan giya na cutar da ma’aikatan cikin jirgi

Ma’aikatan jirgi da aka tattauna da su, sun bayyana yadda fasinjojin ke cin zarafinsu idan sun bugu da giya

Wani bincike da BBC ta gudanar, da aka yi masa lakabi da Panorama, ya gano cewa an samu karuwar mutanen da ake kamawa sun yi mankas da barasa a filin jirgin sama da lokacin da jirgin ya tashi, da kashi 50 cikin 100.

An cafke mutane 387 tsakanin watan Fabrairu shekarar 2016 da watan Fabrairu 2017, idan aka kwatanta da irin wannan lokacin a shekarun da suka gabata da aka kama mutane 255.

Haka kuma kusan rabin ma’aikatan cikin jirgi da BBC ta tattauna da su, sun bayyana yadda mutanen da su kai mankas da barasa ke yi a cikin jigi sun kuma tabbatar da ganin makamancin hakan a filin tashi da saukar jiragen sama na Birtaniya.

 

Tuni kuma hukumar da ke kula da da’a a filin jirgin sama, ta sanar da daukar tsauraran matakai don rage yawan mutanen da ke yin tabargaza a lokacin da suka bugu.

Binciken na Panorama ya ji ta bakin ‘yan sanda, da suka ce cikin mutum 20 da suke gani a filin jirgi, 18 daga ciki a buge suke.

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Trade Body da ke Birtaniya, ya ce zai sanya ya zama doka kan babu wanda zai shiga jirginsu matukar aka gano ya yi mankas da barasa.

Haka kuma, cikin ma’aikatan jirgi 19,000 da aka ji ta bakinsu, 4000 daga ciki sun bayyana yadda fasinjojin da suka bugu da giya ke kokarin kai musu duka, wasu lokutan ma har da kokarin ji musu rauni da sauran na’o’in cin zarafi.

Wata tsohowar ma’aikaciyar kamfanin Virgin Airline, Ally Murphy, da ta bar aiki a watan Oktobar bara, bayan shafe shekara 14 da fara aiki a kamfanin, ta shaidawa BBC cewa ”fasinjoji na wulakantasu, a wasu lokutan ma sai namiji ya taba miki duwawu ko nono ko ya shafa miki kafa, akwai lokacin da wani yake kokarin zura hannunsa cikin Siket dina a lokacin da muke raba musu abinci”.

Daga bisani idan ka kalli fuskokinsu, ka na saurin gane sun yi mankas da barasa ne, abin babu dadi gaskiya.

A watan Yulin bara, hukumar kula da jiragen sama ta Birtaniya ta fitar da wata doka, da kusan daukacin kamfanonin jiragen sama suka rattabawa hannu.

Dokar dai an yi ta ne da nufin gyara, da kuma takaita masu hawa jirgi a lokacin da suka yi markas da barasa.

Da farko dai dokar ta haramtawa duk wanda ya sha giya har ya fita a hayyacinsa shiga jirgi, idan kuma aka samu mutum da take dokar to zai iya fuskantar shekara biyu a gidan kaso.

Haka kuma kantinan da ke sayar da barasa a filin jirgi, an haramta musu saidawa idan ainahin lokacin da ya kamata su tashi ya yi.

Sannan akwai adadin da za su saidawa abokan huldarsu, adadin da ba zai sanya su fita a hayyacinsu har su aikata ba daidai ba.