Wasu masu shirin fim a bakin aiki
A Najeriya gwamnatin kasar ta kuduri wata sabuwar doka ga masu shirya fina-finan Hausa na kasar.
Kudurin dokar da ake kira MOPICON a turance ta kayyade wadanda ya kamata su rika shirya fim a kasar .
To sai dai lamarin bai yi wa wadanda ke gudanar da sana’ar da kuma masu shawar shiga sana’ar dadi ba.
Da dama daga cikin su, sun yi kira da a yi watsi da dokar, a yayin da wasu ke cewa a yi wa dokar gyaran fuska.
Daga cikin abubuwan da dokar ta tanada har da haramtawa matasa ‘yan kasa da shekaru 18 yin fim.
Kuma dokar ta yi tanadin tara har ta naira 100,000 da hukuncin zama gidan wakafi ga duk wani da ya sabawa dokar.
Add Comment