‘YAN FIM MASU TAIMAKO A KANNYWOOD
Daga Darakta Aminu S Bono
ALI NUHU
Wallahi ban san sau nawa ina tare da kai aka kawo maka labarin wane ya shiga matsala kuma ka taimakaba haka kawai kake neman mutum ka ba shi ko bai tambaye ka ba. Wannan al’ada taka sai take birge ni har nake fatan Allah Ya sa nima na taimaki wani dan masana’antar ba tare da ya tambaye ni ba.
IBRAHIM MANDAWARI
Dattijo kuma mai unguwar Mandawari Allah Ya ja da ran mai unguwa, shi mutum ne cikakke sai gashi yau a matakin mai unguwa yake cikin rufin asiri harma ace ana neman taimako kuma ya taimaka wannan shine ake cewa TANADIN GOBE A YAU
ADAM ZANGO
Na san shi sosai kamar yunwar cikina ban san sau nawa ya dauko tsoffin jarumai don yin aiki dasu ba musamman tarayyarsa da darakta Falalu Dorayi. Sune suka canja marigayi IBRO zuwa jarumin da zai tsaya da kafarsa ya kuma sanya farashi daidai da shahararsa cikin mutunci da mutunta juna.
HADIZA GABON
Tunda nake ban taba ganin jaruma mai taimakonta ba, ba zan manta sanda kika je gidan DAUDU GALADANCI ba da irin alherin da kika je da shi ba. Duk da sanda yayi wasan kwaikwayonsa ba ma a haife ki ba ba zan manta taimakon da ki kaiwa abokanan aiki daban daban ba ciki har da ni.