-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Yan Boko Haram Sun Shiga Baga


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rahotanni daga Baga da ke jihar Barno a arewa maso gabashin Najeriya sun nuna cewa mayakan Boko Haram sun shiga garin inda suka kara da sojojin Najeriya.

Wani wanda ya shaida lamarin ya shaida wa BBC cewa mayakan sun afkawa wani babban sansanin soji da ke gefen ruwa a garin na Baga.

Mutumin ya ce da misalin karfe 4 na yamma ne mazauna garin suka fara jin karar makamai inda ake musayar wuta har kusan karfe takwas na dare.

Rundunar sojin Najeriya dai ta sanar cewa mayakan Boko Haram sun kai hari shelkwatar dakarun gamayya na kasashen yankin tafkin Chadi ne da ke Baga a jiya Laraba.

Ta ce dakarunta sun yi fada kan jiki kan karfi don korar mayakan Boko haram din, kuma daya daga cikin sojojin ya rasa ransa a yayin fadan.

Sai dai wanda ya shaida lamarin ya ce mayakan sun shiga garin na Baga bayan wasu daga cikinsu sun yi wa sansanin sojojin kawanya.

Ya kuma ce sojojin da ke cikin garin Baga sun tsere zuwa Munguno.

Ya bayyana cewa mayakan sun kafa tutarsu a babban masallacin Juma’a na garin Baga, kuma ‘yan bindigan ne ma suka ja sallar Asuba.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 657

- Advertisement -

“Muna isa masallaci sai muka ga mutane rike da bindigogi”, a cewarsa.

Ya ce ‘yan bindigan sun yi wa jama’ar garin bayanin cewa su mayakan Boko Haram ne na bangaren Mamman Nur kuma babu ruwansu da dukiyar talaka ko kashe mutane.

“Sun ce su ‘yan kungiyar IS ne, kuma sun ce mu kwantar da hankalinmu”, in ji shi.

A halin yanzu dai, mutumin ya ce ya tsere Maiduguri kuma bai fuskanci wani tashin hankali ba daga gurin ‘yan bindigan duk da cewa a idonsu ya fita ya bar garin.

Rundunar Sojin Najeriya dai ta ce mayakan Boko Haram din na buya a garin Baga da kewaye kuma dakarunta na kokarin gano su.

Rundunar ta kuma ce an tura karin sojojin ruwa da na kasa don samun karin karfin korar ‘yan ta’addan.

#Bbc hausa

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: