‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Hudu Da Sace Mutane 25 A Katsina

0 0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

‘Yan bindiga dauke da manyan bindigogi sun kai hari a garin Mai Bakko da ke cikin karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina, inda suka kashe mutum hudu har lahira suka raunata mutum hudu, wanda yanzu haka suna kwance a Asibiti da kuma sace mata da kananan yara ashirin da biyar.

Dan Majalisar dokokin jihar Katsina, mai wakiltar karamar hukumar Sabuwa a zauren majalisar dokoki, Honarabul Ibrahim Danjuma Macika ya shaidawa RARIYA ta waya dangane da harin da aka kai a garin Mai Bakko a daren jiya Litinin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 782

Dan Majalisar ya kara da cewa ‘yan bindigar sun zo ne da misalin karfe sha biyu na dare, dauke da bindigogi wanda adadin su yana da yawa kowane dauke da bindigogi. Sun kashe mutum hudu har lahira kuma sun raunata mutane hudu, wanda yanzu haka suna kwance a asibitin suna karbar magani. Sun farfasa shaguna da satar dabbobi da dama kuma sun tafi da mutane ashirin da biyar mata da kananan yara, har yanzu muna ci gaba da lissafawa.

Dan Majalisar ya ci gaba da cewa mun yi kokarin kira wo jami’an tsaro, amma sun zo daga baya. Yan bindigar sun kwashe sama da awa daya suna cin karen su ba babbaka har sai da suka tafi suka zo.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: