Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Tara Da Jikkata Wasu Da Dama A Katsina

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

A daren jiya Laraba ne, ‘yan bindiga dauke da bindigogi suka kai hari a garin Unguwar Sarki, da ke gundumar Sheme a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, inda suka kashe mutane tara har lahira da kuma jikkata mutane da dama.

Majiyar RARIYA ta tabbatar Mata cewa mahara sun je garin ne na Unguwar Sarki, da misalin karfe goma sha daya na daren jiya, sun kai sama da awa guda suna ta’addanci a garin nan, babu jami’an tsaron da suka kawo mana dauki, duk da akwai sansanin sojoji a garin Sheme, da bai wuce nisan kilomita ukku ba.

Zuwa yanzu dai da safiyar Nan, mun samu gawarwaki mutum tara, kuma sun jikkata mutane da dama zuwa yanzu ba za mu iya tantance adadin su ba, wasu kuma sun buya ne a cikin daji. Sun kwashe dabbobi da dama. Da safiyar nan za’a gudanar da jana’izar wadanda suka rasu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: