Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Sha Daya Da Kone Rumbunan Ajiyan Abinci Da Dama A Katsina

Dga Jamilu Dabawa, Katsina

A ranar alhamis din da ta gabata ne, yan bindigar suka hari a garin Kabuke, da ke gundumar Runka da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, inda suka kashe mutane goma sha daya, da cinnama rubunan hatsi wuta.

     Majiyar RARIYA, ta shaida mata cewa yan bindigar sun kwashe sama da awa ukku suna ta’addanci a garin, kuma mafi yawancin wadanda suka kashe ‘yan banga ne wadanda suka kawo wa garin dauki ne, sun kashe har mutum goma sha daya, wadanda makwabtan garin Kabuke ne. A garin Jarkuka sun kashe mutum daya da garin Mai Jaura, an kashe masu mutum biyar da Daulai Mutum daya da garin Kwanar Dutse, sun kashe mutum biyu sai kauyen Kabuke sun kashe mutum biyu da kone rambunan abinci akalla hamsin na garin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: