Labarai

'Yan bindiga sun kai hari ofishin EFCC a Abuja

EFCC ta tsananta bincike kan wadanda ake zargi da almundahana tun bayan hawan Shugaba Buhari

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ofishin hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati a Abuja, babban birnin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba da safe, a ofishin hukumar da ke unguwar Wuse Zone 6 a Abujar.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun je wajen ne dauke da bindigogi inda suka fara harbe-harbe a harabar ofishin.
Sai dai har zuwa yanzu hukumar ta ce ba ta san ko su waye suka kai harin ba.
Mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren, ya ce masu gadin ofishin sun fatattaki ‘yan bindigar, amma kafin sannan sun lalata motocin da ke harabar ofishin.
 
Ya kuma ce ‘yan bindigar sun ajiye wata ambulan, wadda ke dauke da sakon barazana ga shugaban sashen da ke bincike a kan almundahana da ta shafi musayar kudaden waje, Ishaku Sharu.
Wannan lamari dai ya faru ne a lokacin da hukumar ke zafafa bincike a kan wadanda ake zargi da almundahana da yin sama da fadi da kudin gwamnati.
Ko a watan Yuni ma wani babban jami’in Hukumar EFCC ya tsallake rijiya da baya a yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude masa wuta a birnin Port Harcourt na jihar Rivers.