Labarai

‘Yan Bindiga Na Bibiyar ‘Dana, Shi Ya Sa Na Cire Shi Daga Makarantar Gwamnati, Cewar El Rufa’i

Daga Jamilu El Hussain Pambegua
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i Ya bayyana muhimmin dalilinsa na cire Yaron sa al Sadiq daga makarantar gwamnati na capital school.

Gwamnan ya ce ya cire dan nasa ne saboda ‘yan bindiga na bibiyar yaron da nufin su yi garkuwa da shi, bayan matakin da ya dauka na cewa gwamnatin sa ba za ta biya kudin fansa ba.

Gwamnan ya kara da cewa a irin wannan yanayin kasancewar dan nasa a makarantar zai jefa sauran daliban makarantar a cikin hadari, hakan ya sa ya bi shawaran hukumomin tsaro ya cire dan nasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: