`Yan Arewa Kar Ayi Gangancin Zaben Su Peter Obi

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

‘YAN AREWA KAR AYI GANGANCIN ZABEN SU PETER OBI

Kamar yadda nake ta kokarin fitar muku da abubuwa akan Peter Obi domin a fahimci hatsarin dake tattare dashi, sannan a fahimci makarkashiyar da ta sa makiyanmu suka hada Peter Obi da Atiku Abubakar domin ya masa mataimakin shugaban ‘kasa, ina sake tabbatar da cewa su Peter Obi ne farkon wadanda zasu fara cin amanar Atiku Abubakar domin su kafa gwamnatin ‘yan Biafra a Nigeria

Talla

Yauma zan sanar daku wani abinda baku sani ba game da Peter Obi.
Akwai wani shahararren kamfanin sarrafa barasa ko giya mai suna HERO LEGER BEER wannan kamfanin giya mallakin Peter Obi ne, shine ya samar da giyan domin ya karrama tsohon madugun kafa ‘kasar Biafra wato Odumegwu Emeka Dim Ojukwu wanda yayi sanadin haifar da yakin basasa a Nigeria mutum sama da miliyon daya suka hallaka, Peter Obi ya samar da wannan kamfanin giya ya kaddamar da giyan a ranar da aka bunne gawar madugunsa Ojukwu domin ya karramashi

Sannan Peter Obi yace a saka tutar ‘yan rajin kafa ‘kasar Biafra a jikin kwalbar giyan domin ya karrama ‘yan Biafra, idan kun duba jikin kwalbar giyan zakuga tutar Biafra ne a jikin kwalbar, sannan rabin kudin riba na giyar da yake shiga masa ya bayar dashi tallafi ga ‘yan Biafra wajen gudanar da ayyukansu wanda ya shafi Redio Biafra biyan ma’aikatansu da jami’an tsaronsu na sirri wanda suke musu leken asirin gwamnatin Nigeria da sauran ayyuka na ‘kungiyar

Bayan nan Peter Obi shine wanda ya mallaki bankin Fidelity (Fidelity Bank), kuma babban asusun ajiyar kungiyar ‘yan rajin kafa ‘kasar Biafra (IPOB) a bankinsa na Fidelity yake, Peter Obi da makamantanshi sune manyan masu ‘daukar nauyin kungiyar domin tabbatar da cewa sun tarwatsa Nigeria sun 6alle sun kafa ‘kasarsu ta Biafra

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 25

Ina ‘yan arewa wadanda suke da burin zasu zabi Atiku Abubakar? to ku san da cewa wakilan inyamurai sun bukaci Atiku Abubakar ya musu alkawarin cewa idan ya kammala wa’adin mulkinsa na tenure daya zai mika musu mulkin imba hakaba to ba zasu goya masa baya ba, akwai yiwuwar sunyi wannan alkawarin a rubuce ya sa hannu domin haka suke yin alkwarinsu tsakaninsu da ‘yan siyasa

Don haka ku ma ‘yan arewa masoya Atiku Abubakar, indai kuna da kishin tabbatuwar Nigeria to ku fito ku kirayi Atiku Abubakar don ya raba hanya tsakaninsa da ‘yan Biafra, idan yaki yin hakan to ku juya masa baya matukar kuna son Nigeria ta kasance a matsayin ‘kasa dunkulalliya

Yaa Allah muna rokonKa da Ka bamu zaman lafiya a Nigeria, sannan Ka haramtawa su Peter Obi zuwa kusa da madafun ikon Nigeria Amin

Daga Assalafy

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: