Yajin Aiki ASUU: Matsalar A Kan Talakawa Take Karewa

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Daga Aliyu Usman Adam
___¥__

Kimanin makonni biyar kenan da kungiyar malaman jami’oin Najeriya, ASUU suka shiga yajin aiki bisa zargin da kungiyar ta yi wa gwamnatin tarayya da gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta yanayin aiki a jami’o’in.

Masu sharhi kan ilimi dai sun yi kira ga gwamnati da malaman jami’o’in da suka rika yin sulhu a tsakaninsu ta yadda ba sai an kai ga shiga yajin aiki ba.
Yawaitar yajin aikin yana jefa harkokin ilimin Najeriya cikin garari.

Talla

Yawancin mutane sun fahimci cewar yajin aiki zai shafi malamai da dalibai ne kawai. Amma batun ya wuce haka, domin iyayen yaran da sauran ma’aikatan jami’o’in ma suna fuskantar cikasa cikin al’amuransu.

A misali, iyayen daliban na kokawa da yadda yajin aikin ke shafarsu, suna cewa ‘ya’yansu kan zama wani nauyi. Su kuma ma’aikatan jami’ar da ba sa koyarwa suna kokawa da yadda ayyukansu ke tsayawa cik duk da cewa su ba sa yajin aiki.

Duk wadannan matsaloli ba ya shafar manyan kasa; wato jami’an gwamnati da manyan masu kudi matsalar tana shafar talakawa ne wadanda su suka fi yawa a cikin al’umma domin kuwa jami’an gwamnati da masu kudi sun tura ‘ya’yansu kasashen waje suna can suna karatunsu ba su da wata matsala.

Talla

Idan kana son ka gane haka a cikin wannan watan ka je filin sauka da tashin jiragen Najeriya babu wadanda za ka gani masu shigowa Najeriya sai ‘ya’yan manya masu karatun jami’a a kasashen waje suna dawowa Najeriya.

Irin wadannan matsaloli a da jama’a na zargin gwamnatin PDP ce take amma fa maganar gaskiya babu bambanci da gwamnatin PDP da na APC idan a wannan bangaren ne.

Wani abu ma wadannan jami’an gwamnatin suna can suna mallakar manyan gidaje a Turai don ‘ya’yansu idan za su yi karunsu a can, kenan babu ranar gyara manyan makarantunmu don kuwa ba ta mu suke yi ba.

Matsalar yajin aikin nan ya zuwa yanzu mutane nawa suka rasa abincinsu tun daga masu shaguna a cikin jami’i’o da masu harkar sufuri(motocin haya) da makamantansu. Ina muka dosa ne?

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 25
Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: