Yahaya Bello Ya Ziyarci Iyalan Jami’in Tsaron Sa Da Ya Mutu A Hatsari, Zai Saya Musu Gidaje A Abuja

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Ismail Karatu Abdullahi

Gwamna jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello Abubakar ya ziyarci iyalan jami’in ɗan sanda daga cikin masu tsaron sa da ya rasa ransa a hatsarin mota domin yi musu ta’aziiya.

Marigayin ya mutu yabbar mata biyu, ƴaƴa biyar da mahaifiya suna zaune a Abuja.

A yayin ziyarar ta ta’aziyyar, Gwamna Yahaya Bello ya tallafawa iyalin da kuɗaɗe tare da yi musu alƙawarin saya musu gidaje biyu a unguwar Kubwa dake babban birnin tarayya Abuja.

A yayin godiya bisa abubuwan alkhairi da gwamnan ya yi musu, matan mamacin biyu sun bayyana gwamnan a matsayin wanda zai yaye musu ƙunci.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 732

Sun bayyana masa cewa, tun can dama mijin su na faɗa musu cewa shine silar haske da zai sauya rayuwarsa.

“Mun gode mai girma gwamna. Dama mai gidan mu ya saba faɗa mana cewa kai ne hasken da zai hasakaka rayuwarsa dan haka ya umarce mu da mu ci gaba da yi maka adu’a. Yanzu ka tabbatar mana da abin da mai gidan mu marigayi yake faɗa mana.

Mun gode da ka haskaka mana rayuwarmu”.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: