Yadda za ku samu tallafin Buhari na biliyan 75 ga ƴan kasuwa


0 524

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shirin bayar da tallafi ga matsakaitan masana’antu wato “MSMEs Survival Fund” na naira biliyan 60, kwatankwacin dala miliyan 156.446 da kuma na c wato Guaranteed Offtake Schemes na naira biliyan 15b, kwatankwacin dala 39.111, shi ne abin da gwamnatin Shugaba Buhari ta samar wa ƴan Najeriya don ƙarfafa musu bayan iftila’in annobar cutar korona.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 631

-Advertisement-

Tambayar da ke zuciyar mutane ita ce ta yaya za su samu wannan tallafi.

Wannan shi karo na biyu da Shugaba Buhari ya fitar shirin rage raɗaɗin da mutane suka samu kansu a ciki sakamakon annobar cutar korona, inda a wannan karon aka ware kuɗi naira biliyan 75.

A cewar gwamnatin, waɗannan shirye-shirye bit=yu an samar da su ne don tallafa wa ƴan kasuwar da annobar cutar korona ta yi wa illa.

Kuɗin dai ba bashi ba ne irin wanda mutane za su biya shi daga baya – tallafi ne kyauta da zai taimaka musu wajen farfaɗowa.

Bari mu ga matajan da mutum zai bi kafin ya amfana da shirin:

Wannan naira biliyan 60 ɗin za a bai wa ƙanana da matsakaitan masana’antu ne don su samu damar biyan ma’aikatansu ko duk wani da ke aiki da su.

Gwamnati ta ce za a raba kuɗin ne ga masana’antu miliyan 1.3 da ƴan kasuwa 35,000 a kowace jiha daga cikin 36 na ƙasar da kuma babban birnin ƙasar Abuja.

Gwamnatin Najeriya za ta bai wa mutum 250,000 damar yin rijistar kasuwancinsu kyauta. zangon farko na wannan tallafi, zai ɗauki wata uku.

Dokoki

  • Dole ka kasance kana da matsakaicin kasuwanci da ke da ma’aikata ko kuma kai kaɗai kake abunka
  • Kashi 45 cikin 100 na waɗanda za su amfana za su kasance mata, yayin da kashi 5 cikin 100 za su kasance masu buƙata ta musamman
  • Idan kamfani ne, dole sai ya yi rijista da Hukumar Rijistar Kamfanoni ta Najeriya, sannan ya kasance yana da a ƙalla ma’aikata uku =, shugaban kamfanin ya kasance ɗan Najeriya ne, sannan sai yana da lambar BVN ta banki
  • Ga masu kasuwanci na ƙashin kansu kuwa, gwamnati ta fi mayar da hankali ne kan masu harkar sufuri kamar direbobin bas-bas da tasi-tasi, da direbobin Uber da Bolt da kuma kaninakawa
  • Sannan masu ƙananan sana’o’i irin masu gyran famfo da birkiloli da masu gyaran wuta da sauran su ma duk sun cancanta

Za a fi mayar da hankali ne kan jihohin Legas da Kano da Abia.

Yadda za ku nemi tallafi

Za a fara rijistar wannan tallafi ranar 21 ga watan Satumban 2020.

Sai ku ziyarci shafinsu na intanet – www.survivalfund.ng inda gwamnati ta wallafa ƙarin bayani.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.