Get New DJ Mixes
Labarai

Yadda wata Malamar asibiti ta kashe marasa lafiya kusan 100

Wata Malamar asibiti ta hallaka marasa lafiya kusan 100 a wata kasa

Niels Hoegel mai shekaru 40 tayi wannan aika-aika ne da gangan

Yanzu haka dai wannan mata tana gidan kurkuku inda ta ke shan dauri

Mun samu wani labari na yadda rashin imani ya sa wata Malamar asibiti ta hallaka marasa lafiya rututu.

 

Wannan Nas Niels Hoegel mai shekaru 40 a Duniya tayi aiki a Birnin Bremen da ke Kasar Jamus inda kwanaki aka daure ta saboda ta yi sanadiyar mutuwar maras lafiya har 2 bayan ta dura masu magani.

Sai dai wannan din somin-tabi ne kamar yadda binciken ‘Yan Sanda ya nuna.

Wani babban Jami’in ‘Yan Sanda Arne Schmidt yace ba mamaki wannan mata tayi sanadiyar arcewa da sama da marasa lafiya 180 a Kasar lahira.

Ana cewa kusan tun bayan yakin Duniya ba a taba samun wanda ya hallaka Jama’a a kasar Jamus haka ba.

Haka kuma kwanan nan kun ji rahoto game da yadda Asibitin koyarwa na Jamia’ar Ahmadu Bello da ke Garin Shika ya kama hanyar sukurkucewa a halin yanzu.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.