Wasanni

Yadda Take Kayawa A Kasuwar Cinikin ‘Yan Wasa

Kamar yadda kasashe da dama suka fitar da jadawalin rana da lokutan da za’a fara buga wasannin rukuni-rukuni haka ma a cikin watan Agusta za’a fara kakar wasa a wasu kasashe a nahiyar Turai, tuni wasu kungiyoyin suka yi nisa wajen daukar ‘yan wasan da za su taka musu rawar gani a kakar wasa ta shekarar 2021 zuwa 2022 mai zuwa.

Wannan dalilin ne ya sa wasu daga cikin kungoyin ke zawarcin ‘yan kwallon da suka taka rawar gani a gasar Euro 2020 wadda aka kammala a farkon wanann watan da wadanda suka yi bajinta a gasar kudancin Amurka wato Copa America a bana.

To sai dai kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo ta bana ta ci karo da koma bayan da cutar korana ta haddasa na karancin kudi tun daga kakar bara kuma hakan yasa ake ganin har yanzu ba za’a kashe kudaden da ake tunani ba a wannan kasuwar.

Sai dai za ka iya fahimtar hakan cewar kungiyoyi da dama na son kara karfinsu domin tunkarar kalubalen gasa mai zuwa, amma ba kudi a kasa, sun gwammace su karbi aron dan wasa ko daukar wadanda kwantiraginsa ya kare kamar dai yadda kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tayi a wannan lokacin.

Kungiyar Barcelona ta dauki ‘yan wasa irinsu Sergio Aguero da takwaransa na Manchester City, Eric Garcia duka daga kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta kasar Ingila bayan kwantiraginsu ya kare da kungiyar.

Har ila yau, kungiyar ta dauki dan wasan gaba daga kungiyar kwallon kafa ta Lyon dake buga wasa a kasar Faransa, Memphis Depay, dan asalin kasar Holland shima a kyauta bayan yaki amincewa da sabuwar yarjejeniya da Lyon din.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, ta dauki ‘yan wasa irinsu Sergio Ramos, wanda ya koma kungiyar daga Real Madrid sai kuma dan wasa Gini Wijnaldum shima ya koma kungiyar daga Liberpool duka a kyauta.

Matashin mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta AC Milan, Gianluigi Donnarumma, wanda ya taimakawa tawagar kasar Italia ta lashe gasar cin kofin turai na Euro 2020 shima ya koma kungiyar bayan kwantiraginsa da AC Milan ya kare.

Sannan kawo yanzu kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig ce kan gaba wajen cin kasuwa mai tsoka da ta kai sama da Yuro miliyan 91, wadda ta dauki Andre Silba kan Yuro miliyan 23 daga Eintracht Frankfurt.

Haka kuma kungiyar ta Jamus ta sayar da Dayot Upamecano ga kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich kan kudi yuro miliyan 42.5 da kuma Ibrahima Konate ga Liberpool da ake cewar kudin cinikin ya kai yuro miliyan 40.

Idan ka auna karfin tattalin arzikin Paris Saint-Germain, amma ta amince ta dauki Sergio Ramos da kuma Gianluigi Donnarumma, wadanda yarjejeniyarsu ya kare a kungiyoyinsu har da Georginio Wijnaldum daga Liberpool zaka tabbatar da cewa kungiyoyi da dama suna fama da kamfar rashin kudi.

Itama Barcelona ‘yan kwallo ukun da ta dauka a bana wadanda kwantiraginsu ya karkare a kungiyoyinsu ciki sun hada da Sergio Aguero da Eric Garcia da kuma Memphis Depay duka a bana.

Kawo yanzu Manchester United ce kan gaba da ta dauki dan wasa daya da tsada, shine Jadon Sancho daga kungiyar kwallon kafa ta Borrusia Dortmund, amma dai za a iya fahimtar yadda cutar korana ta durkusar da cinikin ‘yan kwallo a bana kamar yadda ya faru a bara.

Kungiyoyi da dama sun zabi su dauki aron dan wasa maimakon su mallake shi, sannan wasu na ta kokarin ganin wadanda suke karbar albashi mai tsoka sun rage zuwa wani kaso duk domin tsuke bakin aljihu.

Shima dan wasa Leonel Messi, sai daya rage kashi 50 na cikin albashinsa domin ya ci gaba da zaman kungiyar Barcelona kuma ana fatan a wannan satin za’a sanar da karin kwantiragin dan wasan a hukumance.

Za’a iya cewa wannan koma bayan ya ci karo da cutar korona da ta haddasa, ciki har da yin wasanni ba ‘yan kallo a filayen wasa da sauransu tun daga bara kuma hakan yasa kungiyoyi da dama suka ji jiki ta fannin tattalin arziki.

Amma duk da haka ana sa ran magoya baya za su koma kallon wasanni ido da ido cikin kakar da za’a fara a wasu manyan kasashen Turai daga watan Agusta, wanda hakan zai farfado da wasu abubuwan da aka hakura da su a fannin kwallon kafa, sakamakon bullar Annobar.

#hausaleadership

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: