Labarai Wasanni

Yadda Sunan Ahmad Musa Ya Ceci Rayuwata A Ƙasar Sudan, -Ɗan Nageriya Mai Karatu A Ƙasar Sudań

Sunan Captain Din Nigèria Ahmad Musa Ya Cece Rayuwata A Ƙasar Sudan, -Ɗan Nageriya Mai Karatu A Ƙasar Sudań

 

Wani matashi ɗan Nageriya da ke karatu a ƙasar Sudan inda ake fama da yaƙi, ya bayyana cewa Sunan Captain Ahmed Musa MON ɗan ƙwallon ƙafan Nageriya shi ne ya ceci rayuwarsa daga mutuwa a lokacin da ake tsaka da yaƙi a ƙasar Sudan.

 

Matashin ya saki bidiyo ne da kansa ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta. Inda bayan ganin Bidiyon da Captain Ahmad Musa ya yi ya sanya aka nemo shi domin jinjina masa da fatan alheri.

 

A zantawar Dokin Karfe TV ta yi da shi, matashin ya ƙara da cewa wani soja ne cikin sojojin da su ke yaƙin ya tambaye shi cewa shi ɗan wata ƙasa ne, ya ba shi amsa da cewa shi ɗan Nageriya ne, sai ya ƙara tambayarsa ko ya san Ahmad Musa sai ya sake amsa masa da cewa eh ya san shi ɗan’uwansa ne ma.

 

Daga nan sai ya ƙara da cewa “a sanadiyyar sunan Ahmad Musa sojan ya kula da ni, aka ba ni abinci da ruwa na sha na samu nasara rayuwata ta kuɓuta”. Cewar Matashin.

 

Ahmad Musa wanda a yanzu haka ba ya Nageriya, ya bayyana jin daɗinsa da yadda sunansa ya zama silar ceto rayuwar matashin. Ya sa an nemo shi sun yi waya da Bidiyo Call. Ya kuma bayyana cewa dazarar ya dawo Nageriya zai nemi matashin su gana domin ya yi masa babbar kyauta ta musamman.