Labarai

Yadda Sarkin Sudan Ya Halarci Jana’iza Tare Raka Gawar Sardaunan Kontagora, Alh Sabo Namaska Zuwa Makabarta

Yadda Sarkin Sudan Ya Halarci Jana’iza Tare Raka Gawar Sardaunan Kontagora, Alh Sabo Namaska Zuwa Makabarta

 

Daga Muhammad Ismail Uzange

 

Mai Martaba Sarkin Sudan ya shaidi ɗan’uwan nasa Marigayi Sardauna akan mutumin kirki ne. A cikin alhini Mai Martaba Sarkin Sudan ya yi jawabi a fadar sa bayan dawowa makabarta akan kyawawan ɗabi’u a lokacin da bawa ke raye don Jama’a sun shaidi Marigayi Sardauna da kyawawan dabi’u ga kuma son Jama’a.

 

Allahu Akbar! Dukkan rayuwa wata rana za ta zama gawa, kuma tun kanajin na wani haka za’aji naka kaima, fata dai Allah ya sa mu yi karshe mai kyau “waɗanan na daga cikin hudubar da Mai Martaba Sarkin Sudan ya yi jiya yayin karbar gaisuwar ta’aziyar Marigayi Sardaunan Kontagora Alh. Sabo Namaska.”

 

Maimartaba Sarkin Sudan da kansa ne zai cigaba da karbar gaisuwar ta’aziya a Fadar Masarautar Kontagora zuwa addu’ar uku a gobe Juma’a daga bisani akoma gidan Marigayin dun cigaba da zaman makoki.

 

Allah ya gafartawa Sardauna tare da sauran Musulmi baki daya mu kuma ya kyauta tamu rayuwar ya ha damu gidan Aljannah baki daya, amin.